Ilimi Hasken Rayuwa

Try it Now Firm without compromise. Cancel whenever you want.

Synopsis

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-dabam a duniya, tare da nazari ga irin ci gaban da aka cim ma wajen binciken kimiya da fasaha da ke naman saukakawa Danadam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Biladam. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe.

Episodes

 • Ilimi Hasken Rayuwa - Matashin da ya kera jirgi mara matuki a Kaduna

  Ilimi Hasken Rayuwa - Matashin da ya kera jirgi mara matuki a Kaduna

  04/02/2020 Duration: 09min

  Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya zanta ne da wani matashi dan jihar Kaduna da ya kera jirgin sama mara matuki da ke sarrafa kan shi. Ana iya amfani da wannan jirgin ta fannoni da dama da suka hada da bangaren tsaro da kiwon lafiya da kafofin yada labarai.

 • Ilimi Hasken Rayuwa - Matashin da ya kera mota mai leken asiri a Najeriya

  Ilimi Hasken Rayuwa - Matashin da ya kera mota mai leken asiri a Najeriya

  07/01/2020 Duration: 10min

  Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan mako tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne da wani matashi da ya kera motoci masu sulke da kuma leken asiri domin yaki da bata-gari a Najeriya. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.

 • Ilimi Hasken Rayuwa - Matashin da ya kera injin taimaka wa manoma a Bauchi (2)

  Ilimi Hasken Rayuwa - Matashin da ya kera injin taimaka wa manoma a Bauchi (2)

  24/12/2019 Duration: 10min

  Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya dora ne kan na makon jiya, inda muka tattaunawa da wani matashin injiniya mai fasahar kere-kere a jihar Bauchin Najeriya.

 • Ilimi Hasken Rayuwa - Matashin da ya kera injin taimaka wa manoma a Bauchi

  Ilimi Hasken Rayuwa - Matashin da ya kera injin taimaka wa manoma a Bauchi

  17/12/2019 Duration: 10min

  Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya ci gaba da tattaunawa da daya daga cikin matasan da ke da fasahar kere-kere a Najeriya, inda a wannan karo shirin ya sake lekawa jihar Bauchi don zanta wa da matashin da ya yi kere-kere da dama da suka hada da injin taimaka wa manoma.

 • Ilimi Hasken Rayuwa - Yadda digirin bogi ke barazana ga tsarin ilimin Najeriya 3

  Ilimi Hasken Rayuwa - Yadda digirin bogi ke barazana ga tsarin ilimin Najeriya 3

  10/12/2019 Duration: 10min

  Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Bashir Ibrahim Idris a wannan makon ya dora kan maudu'in makwanni biyu da suka gabata, inda shirin ke tsokaci kan kalubalen da digirin ketare na wa'adin shekara guda ke haifarwa tsarin Ilimi a Najeriya, Ayi saurare lafiya.

 • Ilimi Hasken Rayuwa - Yadda digirin bogi ke barazana ga tsarin ilimin Najeriya 2

  Ilimi Hasken Rayuwa - Yadda digirin bogi ke barazana ga tsarin ilimin Najeriya 2

  04/12/2019 Duration: 10min

  A cikin shirin Ilimi hasken rayuwa na  makon da ya gabata, Bashir Ibrahim Idris ya tabo yadda digirin bogi da daliban Najeriya ke zuwa yi kasashen ketare wani lokacin cikin shekara guda ke matsayin babban kalubale ga tsarin ilimin kasar, ga cigaban shirin.

 • Ilimi Hasken Rayuwa - Yadda digirin bogi ke barazana ga tsarin ilimin Najeriya

  Ilimi Hasken Rayuwa - Yadda digirin bogi ke barazana ga tsarin ilimin Najeriya

  26/11/2019 Duration: 10min

  A cikin shirin Ilimi hasken rayuwa na wannan makon, Bashir Ibrahim Idris ya tabo yadda digirin bogi da daliban Najeriya ke zuwa yi kasashen ketare wani lokacin cikin shekara guda ke matsayin babban kalubale ga tsarin ilimin kasar.  

 • Ilimi Hasken Rayuwa - Matashin Najeriya ya samar da sabuwar fasahar gini 2/2

  Ilimi Hasken Rayuwa - Matashin Najeriya ya samar da sabuwar fasahar gini 2/2

  19/11/2019 Duration: 10min

  Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ci gaba ne kan tattaunawa da wani matashi dan Jihar Bornon Najeriya, wanda Allah ya baiwa fasahar kirkirar wani irin nau'in bulo na gini, da ake amfani da shi ba tare da rodi ko kuma siminti mai yawa ba wajen ginin.

 • Ilimi Hasken Rayuwa - Matashin Najeriya ya samar da sabuwar fasahar gini 1/2

  Ilimi Hasken Rayuwa - Matashin Najeriya ya samar da sabuwar fasahar gini 1/2

  12/11/2019 Duration: 10min

  Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne da wani matashi daga Jihar Bornon Njeriya wanda Allah ya bai wa fasahar kirkirar wani irin nau'in bulo na gini wanda ake amfani da shi ba tare da rodi ko kuma siminti mai yawa ba wajen gine-gine.

 • Ilimi Hasken Rayuwa - Matashin da ke amfani da hannun batir a Gombe (2)

  Ilimi Hasken Rayuwa - Matashin da ke amfani da hannun batir a Gombe (2)

  05/11/2019 Duration: 10min

  Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya dora ne kan na makon jiya, inda ya tattauna da matashin nan da aka yanke masa hannaye a India bayan malaminsa na makarantar allo ya daure hannayen har sai da suka rube.Yanzu haka mashin mai suna Zubairu Yusha'u na amfani da hannun batir.

 • Ilimi Hasken Rayuwa - Matashin da ke amfani da hannun batir a Gombe

  Ilimi Hasken Rayuwa - Matashin da ke amfani da hannun batir a Gombe

  29/10/2019 Duration: 10min

  Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya waiwayi labarin yaron nan mai suna Zubairu Yusha'u da aka yanke wa hannaye bayan sun rube sakamakon daure su da malaminsa na makarantar allo ya yi a jihar Gomben Najeriya. Tuni gwamnati ta dauki nauyin Zubairu zuwa kasar India, inda aka yi masa hannayen da ke aiki da batiri. Kuna iya latsa hoton labarin domin jin yadda Zubairu ke sarrafa hannayensa na batiri. 

 • Ilimi Hasken Rayuwa - Matashin Najeriya da ya yi nasarar kera mota na fatan kera jirgi

  Ilimi Hasken Rayuwa - Matashin Najeriya da ya yi nasarar kera mota na fatan kera jirgi

  22/10/2019 Duration: 10min

  Matashi dan asalin jihar Bauchi a Najeriya da ya yi nasarar kera mota har aka gwada tafiya da ita, ya ce fatansa watarana ya kera jirgin saman da zai tashi.

 • Ilimi Hasken Rayuwa - Yadda masana suka gano maganin cizon maciji a Najeriya

  Ilimi Hasken Rayuwa - Yadda masana suka gano maganin cizon maciji a Najeriya

  08/10/2019 Duration: 08min

  Wasu masana kiwon lafiya a Najeriya sun gudanar da binciken da ya kai ga gano maganin cizon maciji, dai dai lokacin da barazanar kisan da macizai ke yi a ke kara tsananta a kasar.

 • Ilimi Hasken Rayuwa - Maganin saran macizai

  Ilimi Hasken Rayuwa - Maganin saran macizai

  01/10/2019 Duration: 09min
 • Ilimi Hasken Rayuwa - Yadda Jamiar jihar Bauchi ke taka rawa wajen magance kalubalen ilimi a Arewacin Najeriya

  Ilimi Hasken Rayuwa - Yadda Jami'ar jihar Bauchi ke taka rawa wajen magance kalubalen ilimi a Arewacin Najeriya

  17/09/2019 Duration: 10min

  Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Bashir Ibrahim Idris a wannan karon ya duba kalubalen Ilimin da arewacin Najeriya ya fuskanta, matakin da ya tilasta jihohi samar da jami'o'i don habaka harkar ilimin tsakanin al'ummarsu.

 • Ilimi Hasken Rayuwa - Matashi ya kirkiri naurar samar da lantarki mai amfani da hasken rana a Najeriya

  Ilimi Hasken Rayuwa - Matashi ya kirkiri na'urar samar da lantarki mai amfani da hasken rana a Najeriya

  10/09/2019 Duration: 11min
 • Ilimi Hasken Rayuwa - Yadda Bankin Duniya ke tallafawa ilimin yara a Jihar Sokoto ta Najeriya

  Ilimi Hasken Rayuwa - Yadda Bankin Duniya ke tallafawa ilimin yara a Jihar Sokoto ta Najeriya

  06/08/2019 Duration: 10min
 • Ilimi Hasken Rayuwa - Shirin Bankin Duniya na bunkasa ilimi a arewacin Najeriya kashi na (2)

  Ilimi Hasken Rayuwa - Shirin Bankin Duniya na bunkasa ilimi a arewacin Najeriya kashi na (2)

  30/07/2019 Duration: 10min

  Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya ci gaba da tattauna game da tallafin Dala miliyan 100 da Bankin Duniya ya ware domin taimakwa kananan yara musamman mata samun ingantaccen ilimin zamani a arewacin Najeriya.

 • Ilimi Hasken Rayuwa - Shirin Bankin Duniya na bunkasa ilimi a arewacin Najeriya

  Ilimi Hasken Rayuwa - Shirin Bankin Duniya na bunkasa ilimi a arewacin Najeriya

  23/07/2019 Duration: 10min

  Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne game da tallafin Dala miliyan 100 da Bankin Duniya ya ware domin taimakwa kananan yara musamman mata samun ingantaccen ilimin zamani a arewacin Najeriya.

 • Ilimi Hasken Rayuwa - Gwamnatin jihar Yobe a Najeriya ta ayyana dokar ta - baci kan ilimi

  Ilimi Hasken Rayuwa - Gwamnatin jihar Yobe a Najeriya ta ayyana dokar ta - baci kan ilimi

  18/07/2019 Duration: 10min

  A cikin wannan shirin na n'Ilimi Hasken Rayuwa tare da Bashir Ibrahim Idris, za ku ji yadda gwamnatin jihar Yobe a Najeriya ta yunkuro don habaka ilimi, inda har ta ayyana dokar ta - baci kan harkar samar da shi A yi sauraro lafiya.

page 1 from 5

Informações: